Powered By Blogger

Sunday 21 January 2018

Jawabi...!

Da farko dai ka sani
Idan junin ka rãki ne,
magiya ko tsaki dai,
Toh duniyar ma yàyi ce
ma'ajin ta dai júji ne...

Kuma dai ka sani
Ita duniya lilo ce
Ga wanda ya d'ale ya dace
Ga wanda ko bai d'ale ba
Ga 'kadarin sa zai fanshe...

Kuma ka sani,
ita Hali inkiya ce
Idan ka gane tsari ce
Idan ka kula jari ce
Idan ko ka 'kyale musiba ce...

Tabbas duniya Tufa ce,
Malun-malun take ko 'yar shara dai
Mutunci ko, na daga sakun hula ne
Damanga take koma dai 'yar sa'ki ce...

Idan kai malam manomi ne
Toh maza d'au garma, yi hud'a dai
Don dai jinkiri ba taka bace
Idan ka waiga ka hango da saura dai,
toh fa ka sani, sakin 'kota ba naka bane
Don bakka hutu sai randa ka 'kare...

Ka sani fa ita duniya gonar hatsi ce
bata arzi'ki sai an girbe
bata 'kima sai an bushe
Ba kuma a cinta sai an tsince,

Idan ka iya, yau kai ne,
Idan baka iya ba, gobe wani ne
Gurun ka ko laya dai
baya baka hakki nai
Sai dai in kai Sarki ne,
mai mulkin tir da adalci ne...

Ka sani ita dai duniya gida ce
'Kurkuku' ce ga wanda ya dace
ga marar rabo ko aljanna ce...

Idan kai malan maji Izza ne,
mai alfahari da ilimi ne,
kyawu ko dukiya dai
Ko juninka ingiza fasadi ne,
bisa doron 'kasa, koma a daji ne,
Toh ka sani wannan safara ce
Mahayinta dai tsibiri ne,
masau'kin ta ko da kyawu yake a sarari dai,
A zango ko mai ba'kin muni ce...

Hakkun ita duniya Juyi ce
Mazarin ta dai silki ne
Idan ka ninke zai kwaye,
Idan ko ka 'kyale iska zai yaye...

Idan kuma kai bawan buri ne
Toh tabbas ilimi tilas ne
Ha'kuri da dangana ko haddi ne
Muddin ka fito jihadi ne...

Kwarai, ita duniya mayawiya ce
Idan ta sauke wata rana zuma ce
wata ran ko mad'aciya ce...

Don haka idan ka farka cikin rud'u ne
Ka sani matsayar ka bisa buzu ne
Kiranye ta maso 'kibla dai shine
Mafitar ka dai a 'kudirin SA yake...

Ita dai gaskiya hanya ce,
Bata da wãri ko a zance
da zaran an karkata toh an kauce
Ga wanda ya bita da niyyar dace
Ya kame sani ba wani zance
Toh Allah zai masa 'Alam nashareh'

Ita wannar Jawabin dai guzuri ce
Baka biyan ta ko a rance
Sai dai ka mika ta gaba don wani ma ya dace...
Allah yasa mu dace...!

Ibn Adam...

No comments:

Post a Comment